Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Gwamnatin Liberiya Ta Umurci Dakarunta Da Su Nemo Wani Fada Dan Kasar Britaniya... - 2002-05-21


Gwamnatin Liberiya ta umurci sojojinta da su taimaka wajen gano wani fada dan kasar Britaniya, wanda aka bada rahoton bacewarsa tare da wasu makafi su 60.

An ce wannan fada mai suna Garry Jenkins da wadannan makafi fararen hula su 60 sun bace tun ranar 13 ga watan Mayu. Masu magana da yawun kungiyar 'yan tawayen "L.U.R.D." wadda ake kyautata zaton at sace wannan fada da kuma makafin, sun ce fadan yana nan lafiyarsa kalau. An samu rahotannin dake sabawa juna kan inda mutanen da suka bace din suke a yanzu.

Mr. Jenkins shine babban fada na cocin Saint Dominic a garin Tubmanburg, inda aka bada rahoton gwabza fada a tsakanin dakarun 'yan tawaye da na gwamnati.

Fada Jenkins yayi kusan shekaru 20 yana aiki a Liberiya. Cocin tasa ta zamo mafaka ga fararen hular dake tserewa daga sabon fadan da ya barke a garin na Tubmanburg.

Ba a tabbatar da ko sojojin gwamnati ne ko kuma na 'yan tawaye ke rike da wannan gari a halin yanzu ba.

XS
SM
MD
LG