Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Amurka Da MDD Sun Yi Kira Ga Indiya Da Pakistan Da Su Rage Tankiya... - 2002-05-21


Jami'ai daga Amurka da Majalisar Dinkin Duniya, MDD, sun yi kira ga Indiya da Pakistan da su gaggauta rage zaman tankiya a bakin iyakarsu, a bayan karin hare-haren 'yan aware a yankin Kashmir da ake rikici kai, da kuma luguden wutar da sojojin kasashen biyu ke yi daga tsallaken iyaka.

Mai bai wa shugaban Amurka shawara a kan harkokin tsaron kasa, Condoleeza Rice, ta ce shugaba Pervez Musharraf na Pakistan ya tabbatarwa da hukumomin Amurka cewa zai dauki matakan magance 'yan ta'adda.

A halin da ake ciki kuwa, babban sakataren MDD, Kofi Annan, ya ce ya damu sosai da yawan jikkatar da aka yi cikin 'yan kwanakin nan.

Tun da fari, jami'an Pakistan sun yi kira ga wasu kasashen da su lallashi Indiya ta yarda da tattaunawa domin kaucewa yaki gadan-gadan. Ya zuwa yanzu dai, Indiya ta ki yarda da yin tattaunawa har sai a cewarta, ta ga shaidar cewa Pakistan tana daukar matakan murkushe NMusulmi 'yan aware masu samun daurin gindin Pakistan dake kai hare-hare a bangaren Indiya na yankin kashmir.

XS
SM
MD
LG