Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Madagascar Tana Fuskantar Yiwuwar Barkewar Rikicin Soja - 2002-05-23


Shugaban da kotu ta yarda da halalcin ikonsa a kasar Madagascar, Marc Ravalomanana, yayi barazanar daukar matakan soja domin kawo karshen kofar-ragon da aka yi wa Antananarivo, babban birnin kasar.

Ministan tsaro na gwamnatin Mr. Ravalomanana, Jules Mamizara, ya ce za a yi amfani da karfin soja idan har magoya bayan Didier Ratsiraka, wanda shi ma ke ikirarin cewa shine shugaban kasar, ba su dage shingayen da suka kakkafa, suka hana shiga ko fita daga birnin ba, nan da ranar lahadi.

Mr. Ravalomanana yana zaune a babban birnin kasar, wanda aka yi wata da watanni da yi masa kofar-rago, aka tsinke shi daga sauran sassan kasar. Magoya bayan Mr. Ratsiraka sun kakkafa shingaye, suka tarwatsa gadoji akalla 7, a wani yunkuri na hana kai kayayyakin masarufin da ake matukar bukata zuwa babban birnin.

Mutanen biyu suna tabka rikici kan ko wanene ya lashe zaben shugaban kasa na watan Disamba. A watan Afrilu, kotun tsarin mulki ta Madagascar ta sake kidaya kuri'un da aka kada, ta ayyana Mr. Marc Ravalomanana a zaman shugaban kasar. Mr. Ratsiraka ya ki yarda da sake kidaya kuri'un a zaman abinda ya sabawa doka.

Mr. Ravalomanana yana ta kokarin kafa gwamnatinsa, a yayin da gwamnoni da dama masu goyon bayan Mr. Ratsiraka suka bayyana ballewa daga kasar ta Madagascar.

XS
SM
MD
LG