'Yan zanga-zanga su kimanin dubu 20 sun yi cincirindo suka tarbi shugaba Bush a kasar jamus, a daidai lokacin da ya isa can domin tattaunawar kwanaki biyu da nufin karfafa hadin kan kasashen Turai a yaki da ta'addanci a duniya.
An dauki tsauraran matakai jiya laraba a lokacin da Mr. Bush ya sauka a birnin Berlin
Masu zanga-zangar suna bayyana rashin jin dadinsu da manufofin Amurka game da cinikayya, da manufofinta game da rikicin Isra'ila da Falasdinawa, da Iraqi da kuma alkinta muhalli a duniya baki daya. An bada rahoton yin arangama da 'yan zanga-zangar da maraice.
A yau alhamis, shugaba Bush zai yi jawabi gaban majalisar dokokin Jamus. Ana sa ran zai kare manufofinsa na yaki da ta'addanci, zai kuma fadawa 'yan majalisar cewa akidar 'yanci zata samu nasara.
Nan gaba a yau din Mr. Bush zai tashi zuwa Rasha.