Idan Allah Ya kai mu karshen watan nan na Mayu da kuma duk tsawon watan Yuni, Sashen Hausa na Muryar Amurka zai ringa kawo muku rahotanni na musamman kan yadda ake gwabzawa a fagen tamaula a Japan da Koriya ta Kudu.
Gogan naku, Aliyu Mustapha na Sakkwato, tare da sauran wakilan Muryar Amurka dake dukkan filayen wasanni a kasashen biyu, zasu ringa kawo muku labaran abubuwan da suke faruwa cikin fili, da kuma muhimman abubuwan da suke faruwa a bayan fage.
Musamman ma, Aliyu Mustapha zai fi mayar da hankalinsa kan kasashen nan guda biyar da suke wakiltar nahiyar Afirka a wurin wannan wasa na cin kofin kwallon kafar duniya: Nijeriya, Kamaru, Senegal, Tunisiya da Afirka ta Kudu.
A kasance da sashen Hausa na Muryar Amurka a duk cikin shirye-shiryenmu, domin jin rahotanni na musamman kan wannan muhimmin wasa daga bakin Aliyu Mustapha na Sakkwato.