Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kasashen Yammaci Suna Fargabar Za A Yi Yaki Da Makaman Nukiliya A Kudancin Asiya - 2002-05-24


Shugabannin Amurka da na Turai da kuma Rasha, sun roki Indiya da Pakistan da su koma kan teburin shawarwari cikin sauri, yayin da fargaba ke karuwa ta barkewar yaki a tsakanin abokan gabar biyu masu makaman nukiliya.

Shugaba Bush ya ce zaman tankiyar da ake yi a yankin kudancin Asiya na daya daga cikin muhimman batutuwan da ake tattaunawa a lokacin rangadin da yake yi a Turai.

Sakataren harkokin waje Colin Powell yana tare da shugaban a wannan rangadi nasa, kuma a yau Jumma'a yake shirin tattaunawa da shugabannin Indiya ta wayar tarho. A jiya alhamis, yayi magana da shugaba Pervez Musharraf, a wani yunkuri na kwantar da wutar fitina.

Firayim minista Tony Blair na Britaniya, da shugaba Vladimir Putin na Rasha sun tattauna ta wayar tarho jiya alhamis kan bukatar gaggawa da ake da ita, ta yin shawarwarin neman zaman lafiya a tsakanin Indiya da Pakistan.

Wannan kai gwauro da mari da ake yi a fagen diflomasiyya, ya zo a daidai lokacin da jami'an kasashen yammaci suke bayyana fargabar barkewar yaki da makaman nukiliya a yankin kudancin Asiya.

Indiya tana zargin Pakistan da laifin goyon bayan Musulmi 'yan aware, wadanda suka kai hare-hare na ta'addanci a cikin yankin Kashmir dake hannun Indiya. Pakistan ta musanta wannan zargi.

Kasashen biyu sun girka sojoji fiye da miliyan daya a bakin iyakarsu.

XS
SM
MD
LG