Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Shugaba Bush Yana Birnin Moscow Domin Yin Taron Koli Da Shugaba Putin - 2002-05-24


Shugaba Bush yana birnin Moscow, inda idan Allah Ya kai mu a yau Jumma'a zai rattaba hannu kan wata muhimmiyar yarjejeniya ta dakile makamai tare da takwaransa na kasar Rasha, Vladimir Putin.

Yarjejeniyar, zata zabtare kundojin nukiliyar da kasashen biyu ke da shi da kashi biyu cikin uku nan da shekaru 10 masu zuwa.

Mr. Bush ya ce yana da muhimmanci a nunawa duniya cewa Amurka da Rasha suna kulla wata sabuwar dangantaka, kuma a yanzu, su ba abokan gabar juna ba ne.

A daidai lokacin da shugaba Bush ya isa kasar Rasha jiya alhamis domin taron kolin kwanaki hudu da shugaba Putin, zanga-zangar nuna kin jinin Amurka ta barke a biranen Moscow da Saint Petersburg.

Tun kafin nan kuwa a can birnin Berlin, Mr. Bush ya fadawa majalisar dokokin Jamus cewar ana bukatar ci gaba da hadin kai a yaki da ta'addanci a duniya, ya kuma godewa Jamus a saboda goyon bayan da ta bayar a wannan yaki.

Mr. Bush ya jaddada cewa ba za a sakawa 'yan ta'adda ta hanyar biya musu bukatu ba, haka kuma ba za a iya yin watsi da barazanar da suke yi ba.

XS
SM
MD
LG