Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Ana Sa Ran Samun Sakamakon Kuri'ar Raba Gardama Ta Kasar Tunisiya A Yau Litinin - 2002-05-27


A yau litinin ake sa ran sakamakon kuri'ar raba-gardamar da aka gudanar a Tunisiya kan yin gyare-gyare ga tsarin mulkin kasar ta yadda shugaba Zine al-Abidine Ben Ali zai iya shafe shekaru akalla 12 nan gaba kan wannan kujera.

Jami'an zabe suka ce masu jefa kuri'a sun fito da yawan gaske a wannan kuri'ar raba-gardama ta jiya lahadi, inda aka ce sa'o'i da dama kafin a rufe rumfunan zabe, kashi 93 cikin 100 na masu jefa kuri'a sun fito.

Masu jefa kuri'a su miliyan uku da rabi na kasar Tunisiya suna da zabin yarda ko kin yarda da matakin yin gyara ga kusan rabin tsarin mulkin kasar. Masu fashin baki da yawa suna kyautata zaton za a amince da gyare-gyaren.

Kungiyoyin hamayya sun ce gwamnati tana so ne a zartas da gyare-gyaren da zasu bai wa shugaba Ben Ali mai shekaru 65 da haihuwa damar sake tsayawa takara har sau biyu na shekaru biyar-biyar nan gaba. Zabe na gaba zai zo ne a shekara ta 2004, shekaru biyu nan gaba.

Gyare-gyaren da ake son yi ga tsarin mulkin, zasu kawar da tanadin cewa wa'adi uku na shekaru biyar-biyar kawai shugaba zai yi kan mulki, sannan zasu kara yawan shekarun da dan takar ba zai wuce ba zuwa 75.

Wani gyaran kuma, zai bai wa shugabanni kariyar shari'a, ma'ana ba za a taba tuhumarsu a kotu ba, har tsawon rayuwarsu.

Shugaba Zine al-Abidine Ben Ali ya hau kan kujerar mulki a shekarar 1987, lokacin da aka bayyana Habib Bourguiba, wanda yayi shekaru 30 yana mulki ba tare da an kalubalance shi ba a lokacin, a zaman wanda ya tsufa har ya rasa hankalinsa.

A lokacin ne sabon shugaban na Tunisiya ya kawar da tanadin cewa shugaba zai yi mulki har na tsawon rayuwarsa.

Kuri'ar raba-gardamar ta jiya lahadi, ita ce ta farko tun lokacin da Tunisiya ta samu mulkin kai daga Faransa a shekarar 1956.

XS
SM
MD
LG