Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Yi Wa Tsohon Firayim Ministan Madagascar Daurin Talala A Gidansa - 2002-05-28


Ana yi wa tsohon firayim ministan kasar Madagascar daurin talala a gidansa, a bayan wani mummunan farmaki da aka kai a Antananarivo domin kakkabe sauran magoya bayan tsohon shugaban kasar.

Sojoji masu biyayya ga sabon shugaban Madagascar, Marc Ravalomanana, sun kwace sauran ofisoshin dake hannun magoya bayan tsohon shugaba Didier Ratsiraka a babban birnin kasar.

An kashe mutane akalla biyu a lokacin wannan farmakin.

Sojojin sun kama firayim ministan gwamnatin Mr. Ratsiraka, Tantely Andrianarivo, suka tsare shi cikin gidansa.

Ba a san yadda wannan farmaki da kuma tsare tsohon firayim ministan zasu shafi zagaye na biyu na tattaunawar yin sulhu da aka shirya yi gobe laraba da nufin warware rikicin siyasar Madagascar ba.

An shirya gudanar da wannan tattaunawa a Dakar, babban birnin kasar Senegal.

XS
SM
MD
LG