Majiyoyin tsaro na Falasdinawa sun ce sojojin Isra'ila sun sake kutsawa cikin yankin yammacin kogin Jordan, a wannan karo zuwa garin Jenin.
Shaidu sun ce an goce da harbe-harbe a lokacin da tankokin yakin Isra'ila tare da rufa bayan jiragen yaki masu saukar ungulu suka kutsa cikin garin yau talata tun kafin ketowar alfijir.
Wannan farmaki ya zo sa'o'i da dama a bayan da wani Bafalasdine dan kunar-bakin-wake ya kashe 'yan Isra'ila biyu a lokacin da ya tarwatsa kansa a wani jerin kantuna dake wajen birnin Tel Aviv.
Kungiyar dakaru 'yan shuhada'u ta al-Aqsa, wadda ta samo asali daga kungiyar Fatah ta Malam Yasser Arafat, ta dauki alhakin wannan harin. A cikin wata sanarwa, kungiyar ta ce wannan hari fansa ce ta kashe 'yan kungiyar su uku da Isra'ila tayi kusa da garin Nablus a makon jiya.
Kamar yadda ta saba yi, Isra'ila ta dora laifin kai harin a kan shugaban Falasdinawa, malam Arafat da majalisar mulkin kai ta Falasdinawa.
Shugabannin Falasdinawa sun yi tur da harin bam din, amma kuma sun ce watakila za a ci gaba da kai irin wadannan hare-hare har sai lokacin da Isra'ila ta daina kai farmaki cikin garuruwan Falasdinawa.