Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Pakistan Ta Sake Gwajin Makami Mai Linzami... - 2002-05-28


Pakistan ta sake gwajin wani makami mai linzami, a daidai lokacin da tankiya ke kara yin tsanani tsakaninta da Indiya.

Gidan telebijin na Pakistan ya bada labari dazu-dazun nan cewa wannan gwaji na yau talata, ya shafi wani makami mai linzami mai cin gajeren zango.

Wannan shi ne karo na uku da Pakistan take gwajin makamai masu linzami cikin kwanaki hudu.

A ranakun asabar da lahadi, Pakistan tayi gwajin makamai masu linzami, guda mai iya cin tazarar kilomita dubu 1 da 500, dayan kuma mai cin tazarar kilomita 290.

XS
SM
MD
LG