Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Ce Libya Ta Gabatar Da Tayin Biyan Diyyar Dala Miliyan Dubu Dibyu Da Dari Bakwai... - 2002-05-29


An bada rahoton cewa Libya ta gabatar da tayin biyan diyyar dala miliyan dubu biyu da dari bakwai ga iyalan wadanda suka mutu a fashewa da faduwar jirgin saman kamfanin Pan Am mai lambar tafiya 103, wanda bam na 'yan ta'adda ya subuto da shi kasa a Lockerbie a kasar Scotland cikin shekarar 1988.

Wannan labari dai ya fito ne daga bakin lauyoyin dake wakiltar iyalan mutanen a tattaunawa da gwamnatin kasar Libya.

Rahoton ya ce za a biya iyalan kowane mamaci diyyar dala miliyan goma, amma kuma biyan wannan kudi ya dogara ne kan dage takunkumin da Majalisar Dinkin Duniya da Amurka suka sanyawa Libya, da kuma cire sunan Libya daga jerin kasashen da ma'aikatar harkokin wajen Amurka ta ce suna goyon bayan ayyukan ta'addanci.

Lauyoyin suka ce Libya ta ce zata biya kashi 40 cikin 100 idan an dage takunkumin ad MDD ta sanya, ta kara biyan wani akshi 40 daga cikin 100 idan an dage takunkumin ad Amurka ta sanya mata, sannan ta biya sauran kashi 20 cikin 100 idan an cire sunanta daga jerin amsu goyon bayan ta'addanci.

Wani babban jami'in gwamnatin Amurka ya ce babu ruwan gwamnatin Amurka din da tanadin wannan yarjejeniya.

A bara ne wata kotun Scotland ta samu wani jami'in leken asirin Libya da laifin dasa bam din da ya tashi ya tarwatsa jirgin a sama, ya kashe mutane 270.

XS
SM
MD
LG