Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Firayim Ministan Aljeriya Yayi Gargadi Game Da Illar Kauracewa Zabe - 2002-05-30


Firayim ministan Aljeriya, Ali Benflis, ya ce kiraye-kirayen kauracewa zaben 'yan majalisar dokokin da za a yi yau a kasar, suna haddasa kasadar sake jefa Aljeriya cikin yamutsin siyasa.

Wasu manyan jam'iyyun hamayya guda biyu suna kauracewa zaben, yayin da 'yan kabilar Berber masu yawan gaske su ma suna shirin kauracewa zaben na yau.

Mr. Benflis ya shaidawa kamfanin dillancin labaran Reuters cewa kauracewa zaben yana iya haddasa sabbin fadace-fadacen siyasa, tare da kawar da yiwuwar samun shugaba da majalisar dokoki masu tasiri a kasar.

Shugaban 'yan adawa, Said Saadi, ya shaidawa kamfanin dillancin labaran Reuters cewa majalisar dokoki ta gaba ta riga ta mutu tun kafin a zabe ta, ya kuma yi hasashen cewa rikicin siyasa zai barke a kasar.

Masu fashin bakin siyasa sun ce gwamnatin Aljeriya ta yi ko oho da manyan matsalolin cikin gida da kasar ke fuskanta.

Kuri'un neman ra'ayoyin jama'a dai sun nuna cewa jam'iyyar Mr. Benflis ta "National Liberation Front" zata samu kujeru fiye da kowace jam'iyya a zaben na yau, amma kuma ba zata samu rinjayen kujeru ita kadai cikin majalisar ba.

XS
SM
MD
LG