Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Musharraf Yayi Kashedin Cewa Pakistan Zata Maida Martani Mai Zafin Gaske Idan Indiya Tayi Kuskuren Fara Kai Mata Hari - 2002-05-30


Shugaba Pervez Musharraf yayi gargadin cewa Pakistan zata maida martani mai tsananin gaske idan har Indiya ta kuskura ta kai mata hari.

A jiya laraba shugaba Musharraf yayi jawabi ga sojojin dake jinjina masa a kusa da bakin layin da ya raba tsakanin kasashen biyu a yankin Kashmir da ake rikici kai. Ya ce idan har aka kai wa Pakistan hari, to zata maida martani har can cikin tsakiyar Indiya.

A can birnin New Delhi, sakataren harkokin wajen Britaniya, Jack Straw, ya shaidawa manyan jami'an gwamnatin Indiya cewar yayi imani shugaba Musharraf zai yi kokarin biyan babbar bukatar Indiya, watau hana kutsawar 'yan ta'adda zuwa cikin Indiya. A farkon makon nan Mr. Straw ya gana da shugaban na Pakistan. ya bukaci dukkan sassan biyu da su kai zuciya nesa.

Amurka, tayi kashedin cewa wasu 'yan ga-ni-kashe-ni zasu iya yin amfani da wannan lamari wajen haddasa yaki a tsakanin Indiya da Pakistan.

Yau kusan mako biyu ke nan sojojin Indiya da na Pakistan suna musanyar wuta da juna a tsawon layin da ya raba tsakaninsu a Kashmir. Kasashen biyu sun girka sojoji fiye da miliyan guda a bakin iyakar ta su.

XS
SM
MD
LG