Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Shugaba Bush Ya Ce Tilas Musharraf Ya Cika Alkawari - 2002-05-31


Shugaba Bush yayi kira ga shugaba Pervez Musharraf na Pakistan da ya cika alkawuran da yayi na hana 'yan ta'adda tsallakawa cikin bangaren Kashmir dake hannun Indiya domin su kai hare-hare.

A wani yunkuri na kaucewa barkewar yaki a tsakanin Indiya da Pakistan, Mr. Bush ya ce zai tura wani babban jami'in diflomasiyya da kuma sakataren tsaron Amurka, Donald Rumsfeld, zuwa yankin a mako mai zuwa.

Mr. Rumsfeld ya ce lamarin yayi kamarin da ba zai iya cewa komai game da shi a bainar jamaa ba, domin gudun kada a yi kuskuren ba shi wata fassara dabam.

A halin da ake ciki, a yayin da Indiya da Pakistan suke luguden wuta kan junansu a bakin layin da ya raba tsakaninsu a Kashmir, wasu mutane biyu da ake jin cewa 'yan ta'adda ne, sun abka cikin wani sansanin 'yan sandan Indiya a Kashmir, suka kashe mutane uku kafin a bindige su har lahira.

XS
SM
MD
LG