Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Shugaba Musharraf Ya Ce Zai janye Sojojinsa Daga Yammacin Kasar Ya Maida Su Bakin Daga Da Indiya.. - 2002-05-31


Shugaba Pervez Musharraf na Pakistan, ya ce idan har zaman tankiya ya karu tsakaninsu da Indiya, zai janye sojojin da aka girka a bakin iyakar kasar da Afghanistan a yammaci, ya maida su bakin layin da ya raba su da Indiya a Kashmir.

Tun da fari a jiya alhamis, rundunar sojojin Pakistan, da kuma shaidu a bakin iyakar yammacin kasar, sun ce tuni har sojojin sun fara yin kaura.

Har ila yau, shugaban na Pakistan ya ce yaki zai barke ne kawai idan har kasar Indiya ta fara kai musu hari.

A halin da ake ciki, rahotannin kafofin labarai sun ce firayim minista Atal Behari Vajpayee na Indiya ya kira wani taron ba-zata na manyan mashawartansa a daren alhamis.

Daga bisani, ministan tsaron Indiya, George Fernandes, ya ce tilas Indiya ta samu shaidar zahiri nan bada jimawa ba, cewar Pakistan ta daina kyale 'yan ta'adda suna tsallaka bakin iyaka. Har ila yau ya soki kasashen yammaci a saboda yayata yiwuwar barkewar yaki da makaman nukiliya.

XS
SM
MD
LG