Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Mutane Kalilan Suka Fito Domin Yin Zabe A Aljeriya - 2002-05-31


Jami'an Aljeriya sun ce kasa da rabin masu jefa kuri'a na kasar suka kada kuri'unsu a zaben 'yan majalisar dokoki na jiya alhamis. Kauracewar da wasu jam'iyyu suka yi da kuma kashe wasu mutane akalla 20 sun kawar da tasirin zaben.

Ma'aikatar harkokin cikin gidan Aljeriya, ta ce kashi 47 daga cikin 100 na wadanda suka cancanci jefa kuri'a ne kawai suka fito, adadin da shine mafi kaskanci da aka taba gani tun lokacin da kasar ta samu 'yanci daga Faransa a shekarar 1962.

Masu jefa kuri'ar da suka fito ba su kai ko da kashi 3 cikin 100 ba a yankin Kabilye, inda 'yan kabilar Berber suke kauracewa zaben domin nuna rashin jin dadin bambancin da suka yi zargin gwamnati tana nuna musu.

Wasu manyan kungiyoyin adawa ma biyu sun yi kiran da a kauracewa zaben, suna masu hasashen cewa an shirya yin magudi sosai.

A wani gefen kuma, 'yan sanda sun zargi masu kishin addinin Islama da laifin kisan gillar da aka yi a yamma da birnin Algiers, jim kadan kafin a bude rumfunan zabe.

XS
SM
MD
LG