Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

'Yan Sudan Masu Yawa Sun Mutu Yayin Da Suke Kokarin Yin Kaura Zuwa Libya - 2002-06-03


Kamfanin dillancin labaran kasar Sudan, SUNA, ya ce wasu 'yan kasar su 45 dake kokarin yin kaura zuwa kasar Libya, sun mutu a bayan da suka bata a cikin hamada.

Wata sanarwar da gwamnatin lardin Darfur ta Kudu, wadda ke bakin iyakar Sudan da Libya, ta bayar, ba ta bayyana abinda ya kashe su ba, ko kuma lokacin da ka tsinto gawarwakinsu.

Kamfanin dillancin labaran ya ja kunnen sauran 'yan kasar Sudan da su guji kama hanyar zuwa Libya, saboda irin wannan abu yana iya faruwa da su.

'Yan kasar ta Sudan masu yawan gaske sun mutu a lokacin da suke kokarin tsallake hamada a kan hanyarsu ta zuwa neman ayyukan yi masu romo a kasar Libya mai arzikin mai.

XS
SM
MD
LG