Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Tsohon Sarkin Afghanistan Ya Kamu Da Rashin Lafiya - 2002-06-03


Tsohon sarkin Afghanistan ya dakatar da kai ziyara zuwa kasar tasa domin neman hada kan al'ummarta a saboda rashin koshin lafiya.

Wani kakakin fadar tsohon sarkin ya ce Mohammed Zahir Shah, mai shekaru 87 da haihuwa, zai yi tattaki zuwa birnin Kandahar a kudancin kasar da zarar ya samu lafiya, amma bai ce ko za shi Mazar-e-Sharif a arewacin kasar ba, duk da cewa wannan birni yana cikin wadanda tun farko aka tsara zai ziyarta.

Ba a bayyana irin laulayin da sarkinke yi ba.

Tun farko an shirya cewa sarkin zai fara wannan rangadi mako guda kafin a bude babban taron majalisar shawarwari ta kasa da ake kira "loya Jirga" a ranar litinin mai zuwa. Wannan majalisa ce zata zabi gwamnatin rikon kwarya da zata yi mulki na tsawon watanni 18, ko shekara daya da rabi.

Tsohon sarkin bai yanke kaunar karbar mukamin shugaban kasa ba, amma kuma ya ce ba ya son mukamin da ya fi tasiri da iko na firayim minista.

XS
SM
MD
LG