Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Brazil Zata Fara Gwagwarmayar Neman Cin Kofin Duniya Ba Tare Da Shahararren Dan Wasanta Ba - 2002-06-03


A yau litinin Brazil zata fara gwagwarmayar neman cin kofin kwallon kafar duniya ba tare da dan wasan da tafi buga kirji da shi ba.

Kyaftin din Brazil, kuma dan wasan baya mai tasiri Emerson, ya ji ciwo a allon kafadarsa lokacin motsa jiki jiya lahadi, kuma ba zai buga a duk tsawon wannan gasa ba.

Brazil zata gwabza da Turkiyya yau litinin a Koriya ta kudu. A sauran wasannin yau da za a yi daga Japan kuma, Croatia zata kece raini da Mexico, yayin da Italiya, wadda ta dauki wannan kofi har sau uku a baya, zata kara da Ecuador.

A can wani gefen kuwa, 'yan Nijeriya suna can suna tunanin yadda zasu fitar da kitse a wuta a wasannin da suka rage musu, bayan da Ajantina tayi musu ci daya mai ban haushi. Ingila da Sweden sun yi kunnen doki a wan nan rukuni nasu da aka lakabawa suna rukunin mutuwa, ko kuma tungar dodanni.

XS
SM
MD
LG