Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Shugaba Putin Na Rasha Yana Kokarin Sasanta Tankiya Tsakanin Indiya Da Pakistan - 2002-06-03


Shugaba Vladimir Putin na Rasha yayi tayin kokarin shiga tsakanin shugabannin Indiya da Pakistan a wurin wani taron tsaro da za a bude yau litinin a tsohuwar Jamhuriyar Tarayyar Soviet ta Kazakhstan.

Ana sa ran Mr. Putin zai gana dabam-dabam da shugaba Pervez Musharraf an Pakistan da Firayim minista Atal Behari Vajpayee na Indiya domin tattauna rikicin da suke yi a kan yankin Kashmir.

Janar Musharraf yayi marhabin da wannan tayin, ya kuma sake nanata cewar Pakistan ba zata fara kai yaki kan Indiya ba. Amma kuma firayim minista Atal Behari Vajpayee na Indiya ya ce ba ya da wani shiri na ganawa da shugaban Pakistan. Ya ce tilas sai masu kishin addini dake da cibiya a Pakistan sun daina tsallakawa cikin bangaren Indiya na Kashmir suna kai hare-hare kafin a gana.

Kasashen biyu abokan gabar juna, kuma masu makaman nukiliya, sun girka sojoji miliyan guda a bakin iyakarsu, a bayan wasu hare-haren da Indiya ta dora laifinsu a kan 'yan aware masu samun daurin gindin Pakistan.

Iyalan ma'aikatan Majalisar Dinkin Duniya sun fara barin Pakistan, a saboda fargabar cewa yaki yana iya barkewa.

XS
SM
MD
LG