Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Darektan Hukumar Leken Asirin Amurka Ta CIA Zai Gana Da Arafat... - 2002-06-04


Darektan hukumar leken asirin Amurka ta CIA, George Tenet, zai gana da shugaban Falasdinawa, Yasser Arafat, a yau talata, a ci gaba da yunkurin Amurka na farfado da shawarwarin neman zaman lafiya a yankin Gabas ta Tsakiya.

A jiya litinin, Mr. Tenet ya gana da firayim ministan Isra'ila, Ariel Sharon. Wata jaridar Isra'ila ta ce mutanen biyu sun tattauna ne kan yin garambawul a majalisar mulkin kai ta Falasdinawa.

Malam Arafat yana nazarin hanyoyin yin gyara ga majalisar, wadda masu sukar lamirinta suka ce akwai zarmiya da rudu cikinta.

A halin da ake ciki, majalisar zartaswar Falasdinawa ta ce wani dan kishin Falasdinu da Isra'ila take nema zai ci gaba da zama a gidan kurkukun Falasdinawa, duk da umurnin da kotu ta bayar cewar a sake shi. Majalisar ta ce barazanar da Isra'ila keyi ta hana ta sako Ahmed Saadat, wanda kungiyarsa ta PFLP ta dauki alhakin kashe ministan yawon shakatawa na Isra'ila a bara.

A wani labarin kuma, fadar White House ta ce shugaba Bush da firayim minista Ariel Sharon na Isra'ila zasu gana a nan Washington ranar litinin mai zuwa, domin tattauna halin da ake ciki a Gabas ta Tsakiya.

Wannan ziyara zata zamo ta uku da Mr. Sharon ya kawo cikin wannan shekara.

Ganawarsu, zata biyo bayan tattaunawar da aka shirya yi a ranakun Jumma'a da asabar tsakanin Mr. Bush da shugaba Hosni Mubarak na Misra a Camp David, kusa da nan Washington.

XS
SM
MD
LG