Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Wata Kotun Shari'ar Musulunci A Nijeriya Ta Saki Wata Mace Da Aka Ce Tayi Zina, Har Sai... - 2002-06-04


Wata kotun Shari'ar Musulunci a Nijeriya ta saki wata macen da aka yankewa hukumcin kisa bisa laifin zina, domin ta samu damar shayar da diyarta na tsawon watanni 18 nan gaba.

Wata kotun Shari'a a Jihar Katsina ce ta yankewa Amina Lawal hukumcin kisa ta hanyar jefewa. Katsina tana daya daga cikin jihohi 12 na arewacin Nijeriya da suka bullo da Shari'a.

Idan har aka ki yarda da karar da ta daukaka, to ana iya zartas da hukumcin kisa a kan Amina Lawal a shekarar 2004.

Kotunan Shari'a suna daukar macen da tayi jima'i bayan aurenta ya mutu a zaman wadda ta aikata zina.

Mutumin da Amina ta ce shi ne mahaifin diyarta, ya musanta wannan zargi, kuma kotu at sallame shi a saboda rashin shaida.

Lauyan Amina Lawal, Aliyu Musa Yawuri, ya shaidawa kamfanin dillancin labaran Faransa cewa kyale ta ta koma gida domin kula da jaririyarta, alama ce mai karfi cewar kotun zata sallame ta.

XS
SM
MD
LG