Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kwamitin Sulhun MDD Yayi Tur Da Yadda 'Yan Tawayen Kwango Suke Cin Zarafin Wakilan Majalisar - 2002-06-05


Kwamitin Sulhun MDD yayi tur da hare-haren da 'yan tawaye a gabashin Kwango-Kinshasa suke kaiwa cikin 'yan kwanakin nan a kan sojojin kiyaye zaman lafiya na majalisar, ya kuma bukaci da a kawo karshen cin zarafin da ake yi wa jami'an majalisar a can ba tare da bata lokaci ba.

A cikin wata sanarwar da ya bayar jiya talata, shugaban kwamitin sulhun mai ci, jakada Mikhail Wehbe na kasar Syria, ya ce wakilan kwamitin suna yin tur da kokarin 'yan tawaye na gurguta yunkurin wakilan Majalisar Dinkin Duniya a can tare da muhimmiyar rawar ad suke takawa.

A cikin makonnin nan, kungiyar 'yan tawaye mai suna "Rally for Congolese Democracy" dake samun goyon bayan kasar Rwanda, wadda kuma ke rike da biranen Goma da Kisangani a gabashin kasar, ta kori jami'an MDD da dama daga yankin. Har ila yau 'yan tawayen sun ayyana cewar ba su kaunar ganin wakilin babban sakataren MDD, Kofi Annan, a Kwango-Kinshasa, Amos Ngongi.

XS
SM
MD
LG