Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Shugabannin Afirka Suna Shirin Bude Taron Kolin Tattalin Arziki Na Kwanaki Uku - 2002-06-05


Shugabannin siyasa da na 'yan kasuwa na nahiyar Afirka, suna shirin fara ganawa yau laraba a Durban dake Afirka ta Kudu, inda zasu yi taron kolin tattalin arziki na kwanaki uku.

Taron koli na 12 na Dandalin Tattalin Arzikin Duniya a Afirka, zai maida hankali kan sabon Shirin Tattalin Arziki na Raya Kasashen Afirka, ko NEPAD a takaice, wanda ke kokarin shawo kan kasashe masu arziki da su yarda da cewa Afirka wuri ne mai nagarta na zuba jari.

Har ila yau, ana sa ran masu halartar taron zasu tattauna matsalolin dake addabar yankunan nahiyar kamar Zimbabwe da Kwango-Kinshasa. An dage shawarwarin neman zaman lafiyar Kwango da aka shirya gudanarwa makon da ya shige a kasar Zambiya har sai illa ma sha Allahu, a saboda an kasa sanin ko su wa da wanene zasu halarta.

XS
SM
MD
LG