Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Rumsfeld Ya Ce Tankiyar Indiya Da Pakistan Ba Ta Raunana Yaki Da Ta'addanci A Afghanistan - 2002-06-05


Sakataren tsaron Amurka, Donald Rumsfeld, ya ce tankiya a tsakanin Indiya da Pakistan tana kawar da hankali, amma kuma ba ta gurgunta kokarin da Amurka take yi wa jagoranci na yaki da ta'addanci a kasar Afghanistan ba.

Mr. Rumsfeld ya ce Pakistan ta janye wasu soijoji 'yan kalilan daga bakin iyakarta da Afghanistan, ta tura su kudu zuwa bakin iyakarta da Indiya, amma kuma ya ce wannan bai shafi akasarin sojojin Pakistan wadanda suke farautar 'yan al-Qa'ida da na Taleban ba.

Sakataren tsaron na Amurka zai fara ziyarar Indiya da Pakistan a ranar lahadi, amma kuma ya ce ba zai taka rawar mai shiga tsakani ba. A yau laraba Mr. Rumsfeld zai fara ziyara a kasashen waje, inda zai fara yada zango a birnin Brussels domin tattauna yaki da ta'addanci da kuma makaman kare-dangi da kawayen Amurka na kungiyar kawancen tsaron NATO.

XS
SM
MD
LG