Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Bam Ya Kashe Mutane Akalla 14 A Isra'ila - 2002-06-05


'Yan sandan Isra'ila sun ce mutane akalla 14 sun mutu, wasu guda 45 sun ji rauni, wasunsu mummunan rauni, a lokacin da aka kai hari kan wata motar safa da bam din da aka boye cikin wata motar dabam a arewacin Isra'ila.

Suka ce bam din dake boye cikin motar ya tashi a jikin motar safar a daidai lokacin da take kokarin tsayawa kusa da garin Megiddo, kilomitoci da dama daga bakin iyaka da yankin Yammacin kogin Jordan.

Motar safar ta kama da wuta. Shaidu suka ce wutar ta rutsa da wasu fasinjoji da ransu cikin motar safar.

Firayim ministan Isra'ila, Ariel Sharon ya kira taron gaggawa na manyan ministocinsa domin tattauna martanin da zasu maida game da harin, wanda ya faru yau laraba da safe, a daidai lokacin da ake zuwa aiki.

A can birnin Beirut, wani gidan telebijin ya bada rahoton cewa kungiyar 'yan kishin Falasdinu ta Islamic Jihad, ta dauki alhakin kai harin.

XS
SM
MD
LG