Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

MDD Ta Ce Kogunan Karkashin Kasa Na Afirka Zasu Iya Warware Matsalar Ruwa A Nahiyar - 2002-06-07


MDD ta ce masana kimiyyar sigar ruwa a karkashin kasa suna fatan yin amfani da manya-manyan kogunan karkashin kasa na Afirka a wani yunkuri na warware matsalar karancin ruwa a nahiyar.

A cikin wata sanarwar da ta bayar jiya alhamis, Hukumar Ilmi, Al'ada da Kimiyya ta MDD, UNESCO, ta ce masana sigar ruwan karkashin kasa daga kasashe 20 sun gudanar da aikin safiyo na farko na kogunan karkashin kasa da suka ratsa kasashe dabam-dabam a nahiyar Afirka. UNESCO ta ce a cikin makon nan kwararrun suka gudanar da taron kwanaki biyu a Tripoli, babban birnin Libya.

Hukumar ta UNESCO, ta ce daya daga cikin irin wadannan koguna, girmansa ya kai fadin kasar Jamus, kuma yana kwance daruruwan mitoci daga doron kasa a karkashin hamadar kasashen Libya, Masar, Chadi da kuma Sudan. Ta ce kwararrun sun gano irin wadannan manyan koguna har guda 20 da suka ratsa kasashe dabam-dabam na Afirka.

Hukumar UNESCO ta ce wannan ruwa mai yawan gaske dake kwance a karkashin kasa zai iya taimakawa miliyoyin jama'a.

XS
SM
MD
LG