Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Shugaba Bush Ya Bada Shawarar Kafa Sabuwar Ma'aikatar Tsaron Cikin Gida - 2002-06-07


Shugaba Bush ya roki majalisar dokoki da ta taimaka masa wajen kirkiro da sabuwar ma'aikata mai kujera a majalisaqr zartaswa, wadda zata kula da tsaron cikin gida.

A cikin jawabin da yayi ta telebijin ga al'ummar Amurka, Mr. Bush ya ce ana bukatar yin muhimman sauye-sauye na ba-zata a tsarin ayyukan gwamnati, domin takalar barazanar 'yan ta'adda a cikin karni na 21.

Ya ce sabuwar ma'aikatar zata karbe kula da wasu hukumomin gwamnati, ciki har da hukumar tsaron bakin gabobin tekun Amurka, da hukumar kwastan, da ta kula da shige da ficen baki, da masu gadin bakin iyakoki da kuma hukumar agajin gaggawa.

Har ila yau ya ce wannan sabuwar ma'aikata zata nazarci dukkan bayanan leken asirin da Amurka ke tarawa a kowace rana, domin fito da rahoto ko wace rana kan irin barazanar da Amurka take fuskanta.

Wannan shawara ta kafa sabuwar ma'aikatar, ta zo a daidai lokacin da ake ta samun rahotannin dake cewa an samu kura-kuran sarrafa bayanan leken asiri kafin hare-haren ta'addanci na ranar 11 ga watan Satumba.

Tilas sai majalisar dokoki ta amince da kafa sabuwar ma'aikatar.

XS
SM
MD
LG