Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Yunkurin Yin fashin Jirgin Sama A Ethiopia Ya Ci Tura - 2002-06-10


Kafofin labarai a kasar Ethiopia sun ce jami'an tsaro sun kashe wasu mutane biyu wadanda suka yi yunkurin fashin wani jirgin saman fasinjan kasar.

Rahotannin kafofin labaran sun ambaci jami'an kamfanin safarar jiragen saman "Ethiopian Airlines" suna fadin cewa su wadannan 'yan fashi dake dauke da wukake, sun yi kokarin fashin wannan jirgi jiya lahadi, a lokacin da yake zirga-zirgar cikin gida zuwa Addis Ababa, babban birnin kasar.

A lokacin, wannan jirgi yana dauke da fasinjoji 42.

Ba a san dalilin mutanen na kokarin yin fashin jirgin saman ba.

XS
SM
MD
LG