Babban jami'in cinikayyar Amurka, Robert Zoellick, ya bayyana cewa kauracewa kayayyakin da aka sarrafa a Amurka a saboda fifikon da ake ganin Amurka tana bada Isra'ila a Gabas ta Tsakiya, zai yi illa ga talakawan Misra fiye da Amurka.
Mr. Zoellick, wanda ke ziyara a Misra, ya shaidawa taron 'yan jarida a birnin al-Qahira cewa kauracewa kamfanonin Amurka, tamkar raunana kai da kai ne ga Misrawa, saboda Misrawan ne ke yi wa kamfanonin aiki, kuma suna da mukamai masu kyau.
Yawan kiraye-kirayen kauracewa kayayyakin da aka kera ko aka sarrafa a Amurka suna kara yaduwa cikin 'yan watannin nan, yayin da kokarin wanzar ad zaman lafiya a Gabas ta Tsakiya ya cije.
Mr. Zoellick, wanda shine babban jami'in shawarwarin cinikayya na shugaba Bush, ya yarda cewa kauracewar tana tayar da hankulan kamfanonin Amurka a saboda tana haddasa yanayi mai wuya na gudanar da ayyukansu.