Sabon shugaban kasar Mali, ya nada Mohammed Ag Amani, wanda yayi minista a zamanin mulkin soja, a zaman firayim minista.
Jiya lahadi a birnin Bamako, babban birnin kasar, shugaba Amadou Toumani Toure, wanda shi kansa ya taba zama shugaban gwamnatin mulkin soja, ya bada sanarwar nadin.
Malam Mohammed Amani, masanin tattalin arziki, ya rike mukamai dabam-dabam na minista a zamanin gwamnatin Janar Moussa Traore.
Kamfanin dillancin labaran Faransa, ya ce sabon firayim ministan ya kuma rike mukamin jakada a Morocco da Belgium.
A ranar asabar aka rantsar da Mr. Toure a zaman shugaban kasa na shekaru biyar. Ya fara hawa kan kujerar shugabancin kasar a bayan juyin mulkin sojan da yayi wa shugaba Traore a shekarar 1991. Daga nan ya jagoranci kasar zuwa ga mulkin dimokuradiyya.