Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Sojojin Isra'ila Sun Kutsa Cikin Ramallah - 2002-06-10


Jami'an Falasdinawa sun ce tankokin yakin Isra'ila fiye da saba'in sun kutsa cikin garin Ramallah a yankin Yammacin kogin Jordan, abinda ya haddasa barkewar kazamin fada.

Suka ce sojojin Isra'ila sun kewaye hedkwatar shugaban Falasdinawa, Yasser Arafat. Jami'an Isra'ila sun ce sun kai wannan farmaki ne domin damko mutane da dama da suke farauta.

Yau litinin da asubahi sojojin na Isra'ila suka fara kutsawa cikin garin Ramallah, sa'o'i a bayan da shugaban Falasdinawa ya rage girman majalisar zartaswarsa, ya kuma nada wani a matsayin ministan harkokin cikin gida, duka a wani bangare na yin gyara ga majalisar mulkin kai ta Falasdinawa.

Malam Arafat ya nada Abdel Razak Yehiyeh a zaman ministan harkokin cikin gida domin yin garambawul ga hukumomin 'yan sanda da na leken asirin Falasdinawa.

XS
SM
MD
LG