Shugaba Charles Taylor na Liberiya, yayi ikirarin samun nasara a wani farmaki kan 'yan tawaye a arewacin kasar, yana mai fadin cewa sojojinsa sun kwace garin Kolahun daga hannun 'yan tawaye.
Amma wani kakakin kungiyar 'yan tawaye ta "Liberians United for Reconciliation and Democracy" ya shaidawa kamfanin dillancin labaran Reuters cewa babu gaskiya a cikin ikirarin na Mr. Taylor, yana mai fadin cewa kungiyarsu ta samu nasarori kan sojojin gwamnati da na 'yan banga masu taimaka mata a yankin.
Shugaba Taylor ya fadawa 'yan jarida a Monrovia, babban birnin kasar, cewar kama wani rumbun tara makamai na 'yan tawaye a Bopolu, ya bai wa sojojin gwamnati damar samun nasarar kame garin Kolahun.
Shugaban ya kara da cewa yanzu sojojin na gwamnati sun dirkaki 'yan tawaye a garin Tubmanburg, wanda ke arewa da babban birnin kasar.
Babu wata kafa ta tabbatar da gaskiyar ikirarin shugaban.
Dubban mutane sun gudu daga gidaje da garuruwansu a saboda fada na baya-bayan nan a kasar Liberiya.