Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

A Yau Faransa Zata San Makomarta A Fagen Gasar Cin Kofin Kwallon Kafar Duniya - 2002-06-11


Za a buga wasanni hudu yau talata a ci gaba da gasar cin kofin kwallon kafar duniya a Koriya ta Kudu da Japan, ciki har da wasan da zai shata makomar kasar Faransa wadda ke rike da kofin, a cikin gasar ta bana.

Faransa zata kara da Denmark a filin wasa na Mun-Hak a Koriya ta Kudu, yayin da kasar Senegal ba-da-mamaki zata kara da Uruguay a Suwon, duka a rukunin farko. Senegal da Denmark duk suna da maki hurhudu a wannan rukuni, yayin da Faransa da Uruguay suke da maki daddaya. Faransa tana iya shiga zagaye na biyu idan har ta doke Denmark, sannan kuma Senegal ta doke Uruguay ko kuma tayi kunnen doki da ita.

Haka kuma, a yau ne za a san wadanda zasu yi gaba, da wadanda zasu tattara 'yan komatsansu su nufi gida a rukuni na 5 ko "E". Za a murza gashin baki sosai idan har Kamaru da Jamus suka yi kunnen doki a filin wasa na Shizouka a Japan, kuma idan har Ireland ta doke Saudi Arabiya, kamar yadda ake ganin tana yiwuwa. Idan har hakan ya faru, to za a samu kasashe uku cur, ko wacce da maki biyar-biyar, saboda haka, yawan kwallo ne zai tantance biyun da zasu shige, da guda dayar da zata ciza yatsa ta yarfar da gumi ta doshi gida.

A jiya litinin dai, Amurka tayi kunnen doki 1-1 da Koriya ta Kudu, kuma dukkansu suna saman rukuninsu. Yanzu dai an yi waje-rod da Poland bayan da Portugal ta lakkada mata duka da ci 4 da wofi.

Tunisiya kuma, tayi kunnen doki, 1-1, da Belgium. Dukkan kasashen biyu dai suna bayan japan da Rasha a rukuninsu na 8 ko "H".

XS
SM
MD
LG