Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Bush Ya Ce Yasser Arafat Ya Ba Shi Kunya - 2002-06-11


Shugaba Bush ya bayyana karayarsa da iya jagorancin shugaban Falasdinawa Yasser Arafat, yana mai fadin cewa ana bukatar karin gyare-gyare a majalisar mulkin kai ta Falasdinawa.

Mr. Bush ya bayyana wannan jiya litinin a lokacin da yake ganawa, a nan birnin Washington, da firayim ministan Bani Isra'ila, Ariel Sharon, mutumin da shi ma ya ce yana shakkar iya shugabancin Malam Arafat.

Mr. Bush ya kuma ce Isra'ila tana da ikon kare kanta.

Shugabannin biyu sun gana a daidai lokacin da tankokin Isra'ila suka kewaye hedkwatar Malam Arafat dake garin Ramallah a karo na biyu cikin mako guda.

Wani kakakin fadar White House, ya ce Amurka ta gamsu da tabbacin da Isra'ila ta bayar cewa wannan farmaki na takaitaccen lokaci ne. An kama Falasdinawa fiye da 20 da ake zaton ko masu kishin Falasdinu ne.

XS
SM
MD
LG