Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Indiya Zata Dage Takunkumin Hana Jiragen Saman Fasinjan Pakistan Shiga Cikin Samaniyarta - 2002-06-11


Indiya ta ce zata dage dukkan haramcin da tayi wa jiragen saman fasinjan kasar Pakistan na shiga cikin samaniyarta.

Wannan mataki ya zo kwana guda a bayan da gwamnatin Indiya ta ce zata fara daukar matakan sassauto da zaman tankiya tsakaninta da abokiyar gabarta Pakistan mai makaman nukiliya.

Ma'aikatar harkokin wajen Indiya ta ce zata kara daukar wasu matakan idan ta ga alamun cewa Pakistan tana hana masu kishin addini tsallakawa zuwa cikin Indiya.

Ma'aikatar harkokin wajen Amurka, da shugaba Pervez Musharraf na Pakistan sun yi marhabin da matakin da Indiyar ta dauka jiya litinin. Amma kuma Shugaba Musharraf ya ce har yanzu ba a fita daga cikin hadarin yaki ba, muddin aka ci agba da girka sojojin a bakin iyakar Indiya da Pakistan.

XS
SM
MD
LG