Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kasadar Bala'in Yunwa A Nahiyar Afirka Ita Ce Matsalar Karancin Abinci Mafi Tsanani A Duniya - 2002-06-12


Shugaban hukumar samar da abinci ta MDD ya ce yankin kudancin Afirka yana fuskantar abinda ya kira matsalar abinci mafi tsanani yanzu haka a duk fadin duniya.

A lokacin da yake magana wajen taron kolin kasashen duniya kan batun abinci a birnin Rum a kasar Italiya, James Morris ya ce mutane miliyan 13 a kasashe 6 a yankin kudancin Afirka suna fuskantar kasadar bala'in yunwa.

Ya roki kasashen duniya da su bada agajin abincin gaggawa na miliyoyin daloli domin kaucewa yunwa a kudancin Afirka.

A yau laraba aka shiga rana ta uku da fara wannan taron kolin kwanaki hudu.

Hukumar samar da abincin ta duniya ta ce kasashen Malawi, Zimbabwe, Lesotho, Swaziland, Zambiya da Mozambique suna fuskantar karancin abinci mai tsananin gaske a saboda dalilan da suka hada da fari, ambaliyar ruwa, kasawar gwamnati, da kuma annobar cutar kanjamau, ko AIDS ko kuma SIDA.

Shugabannin kasashen duniya da dama da kuma jami'ai suna halartar wannan taron koli. Hukumar samar da abincin ta MDD tana da membobi 182.

Tun da fari a jiya talata, hukumar tallafawa kasashe masu tasowa ta Amurka, USAID, tayi alkawarin bada karin agajin ton dubu 195 na masara, da wake, da man girki, da wasu kayan abincin domin tallafin gaggawa a kudancin Afirka.

Amma kuma duk da haka, kasashe da dama a zauren taron sun soki lamirin Amurka a saboda dokar da ta kafa ta bada tallafin farashi ga manoman Amurka.

Jami'ai daga kasashen Canada da Latin Amurka sun ce wannan cin zarafi ne ga akidar walwalar kasuwanci, kuma zai gurbata farashin kayan amfanin gona a kasuwanni.

XS
SM
MD
LG