Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

MDD Tana Binciken Kashe-Kashen Kare Dangi Na Kabilanci A Kwango-Kinshasa - 2002-06-12


Jami'an soja 'yan kallo na Majalisar Dinkin Duniya, MDD, a Kwango-Kinshasa, sun fara gudanar da bincike game ad zargin cewa an kashe mutane fiye da dubu biyu a fadace-fadacen kabilanci a yankin arewa maso gabashin kasar.

Jami'an MDD sun fada a jiya talata cewar suna shirin ci gaba da wannan aikin bincike, duk da barazanar da aka yi wa ma'aikatan Majalisar da na kungiyoyi masu zaman kansu a wannan yanki, inda kabilun Lendu da Hema suke zaune.

Jami'an na MDD suka ce 'yan kabilar Hema 'yan tsiraru sun zargi kabilar Lendu mai rinjaye a yankin, tare da 'yan tawaye masu samun goyon bayan Uganda, da laifin kai musu farmaki.

A wani labarin kuma, MDD ta ce zata tura wata mai bincike zuwa kasar ta Kwango-Kinshasa, domin gano gaskiyar zargin cewa a watan da ya shige, 'yan tawaye sun kashe mutane har dari biyu a birnin Kisangani dake arewacin kasar.

A cikin sanarwar da ta bayar jiya talata, majalisar kwararriya a fannin kare hakkin bil Adama, Asma Jahangir, zata gana da jami'an MDD da na gwamnatin Kwango-Kinshasa a birnin Kinshasa.

Daga nan zata yi tattaki zuwa biranen Goma da Kisangani, wadanda ke hannun 'yan tawaye amsu samun goyon bayan Rwanda. Ms. Jahangir tana shirin ganawa tare da yin tambayoyi ma shaidu da mutanen da suke zargin an keta hakkinsu.

Jami'an MDD sun zargi kungiyar "Congolese Rally for Democracy" da laifin yin kashe-kashen gilla a ciki da wajen birnin Kisangani a watan da ya shige, a bayan da aka yi wani yunkurin da bai samu nasara ba na tayarwa da kungiyar kayar baya.

XS
SM
MD
LG