Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

A Yau Alhamis Majalisar Loya Jirga Zata Zabi Shugaba - 2002-06-13


A yau alhamis ake sa ran wakilan dake halartar babban zauren shawarwari na kasa baki daya da ake kira Loya Jirga a Afghanistan, zasu zabi shugaban kasa, a bayan da aka wuni jiya laraba ana tabka muhawara mai sosa zuciya.

na akyautata zaton za a zabi shugaban gwamnatin rikon kwarya na yanzu, hamid Karzai, bisa wannan mukami, a bayan da tsohon sarkin Afghanistan, Mohammed Zahir Shah, da tsohon shugaban kasa Burhanuddin Rabbani, suka ce ba zasu nemi wannan mukami ba.

A bayan wannan kuma, tilas ne wakilan dake halartar taron su zabi wakilan gwamnatin da zata jagoranci kasar a cikin shekara guda da rabi mai zuwa.

Ajandar taron ta wargaje jiya laraba, a bayan da wakilai suka ringa tashi daya bayan daya domin yin tambaya, ko jawabi ko kuma gabatar da kuka. An yi ta tafa ma wani wakili mai suna Safar Mohammed, lokacin da ya ce kwamandojin kungiyoyin sojan sa kai sun cika zauren taron har ma bai san ko wannan majalisar Loya Jirga ce, ko kuma majalisar sojoji ba.

A halin da ake ciki, kamfanin dillancin labarai na Reuters ya bada labarin cewa wakilai har 70 ne suka shura takalmansu suka fice daga zauren taron, suna korafi kan abinda suka kira rashin bada wakilai 'yancin jefa kuri'a tsakani da Allah a game da makomar kasar.

Daga bisani, mutane sun tsorata na wani dan karamin lokaci a wani hotel an birnin Kabul, lokacin da wata bindiga mai zazzage wuta ta wani sojan kiyaye zaman lafiya dan kasar Jamus, tayi barin wuta bisa kuskure. Bindigar ta huda ramuka shida jikin wata motar gidan telebijin, amma kuma babu wanda ya ji rauni.

XS
SM
MD
LG