Ma'aikatar tsaron Amurka, Pentagon, ta ce sojoji uku sun mutu jiya laraba da maraice a lokacin da wani jirgin mayakan Amurka ya fadi a yankin gabashin Afghanistan.
Ma'aikatar ta Pentagon ta ce sauran mutane bakwai dake cikin jirgin sun kubuta da raunukan da suka kama daga karaya a kafa zuwa tabo da kwarzane.
Jirgin ya fadi a lokacin da ya tashi kusa da madatsar ruwa ta Bande Sardeh, kilomita 60 a kudu maso yamma da garin Gardez. Sojojin Amurka sun jima suna farautar mayakan al-Qa'ida da na Taleban a wannan yankin.
Pentagon ta ce ba a san musabbabin faduwar wannan jirgi ba, amma kuma ta ce babu wata alamar cewa an harbo shi ne.
Wannan jirgi samfurin MC-130, wanda ake wa lakabi da sunan "Combat Talon", an kera shi ne musamman domin kutsawa da sojoji zuwa can cikin yankin abokan gaba.