Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Mullah Omar Ya Ce Bin Laden Yana Nan Da Rai... - 2002-06-13


Wata sananniyar jaridar kasar Rasha da ake mutuntawa sosai, ta ce dan ta'addar da aka fi nema ruwa a jallo a fadin duniya, Osama bin Laden, yana nan da rai, yana kuma kulla kai hare-hare kan Amurka.

Jaridar ta Rasha mai suna " Argumenty i Fakty" wadda ake bugawa mako-mako, ta ce ta samu wannan bayani ne ta hanyar amsar wata wasikar gizo, ko Email, wadda ta samu daga hannun wani dake kiran kansa Mullah Mohammed Omar, shugaban hambararriyar gwamnatin 'yan Taleban ta Afghanistan.

Jaridar ta ce ta aike da tambayoyi a watannin baya ga shi Mullah Omar ta hannun wasu masu shiga tsakani, cikinsu har da tsoffin jami'an Taleban da larabawa 'yan jarida.

Babu hanyar tabbatar da sahihancin wannan wasikar gizo, haka kuma jaridar ba ta bada bayanin inda Mullah Omar yake a yanzu ba.

XS
SM
MD
LG