Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Za A Ci Gaba Da Cike Gurabu A Zagaye Na Biyu Na Kwallon Duniya - 2002-06-13


Kasar Italiya, wadda sau uku tana lashe kofin duniya, zata kara da Mexico, yayin da Croatia zata kece raini da Ecuador a rukuni na 7, inda Italiya take fatan samun tsallakewa zuwa zagaye na biyu.

Kasar Brazil wadda ta lashe wannan kofi har sau hudu kuma, zata gwabza da Costa Rica, yayin da Turkiyya zata kara da China, wadda wannan shine karon farko da take zuwa gasar.

Italiya zata yi kokarin farfadowa daga kashin da ta sha a hannun 'yan Croatia a makon jiya da ci 2-1, idan ba haka ba kuwa, to watakila 'yan wasanta zasu nemi hanyar komawa Rum. Mexico take saman wannan rukuni, yayin da Italiya ke bayanta. Ecuador dai tuni aka yi waje-rod da ita.

A jiya laraba, Paraguay da Ingila da Sweden duk sun wuce zuwa zagaye na biyu.

XS
SM
MD
LG