Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Sojojin Isra'ila Sun Kai Karin Hare-Hare Cikin Yankunan Falasdinawa... - 2002-06-14


Sojojin Isra'ila sun kama karin mutane a lokacin hare-haren da suka kai cikin yankunan Falasdinawa.

An bada rahoton kama mutane fiye da ashirin da ake jin cewa 'yan kishin Falasdinu ne, a lokacin da sojojin Isra'ila suka kai hare-hare jiya alhamis a garin Tubas dake arewacin yankin Yammacin kogin Jordan.

An raunata Falasdinawa uku da sojojin Isra'ila biyu a musanyar wutar da aka yi da bindigogi.

A halin da ake ciki, shugaban Falasdinawa, Yasser Arafat, ya kira taron farko an sabuwar majalisar zartaswar da aka rage girmanta a garin Ramallah.

Malam Arafat ya ce nan bada jimawa ba zai bada sanarwar ranakun gudanar da zabubbukan shugaba, 'yan majalisar dokoki da na birane da garuruwa.

Jami'an ma'aikatar harkokin wajen Amurka, wadanda suka ce ba su gamsu da garambawul din da Malam Arafat yayi wa majalisar zartaswarsa ba, sun yi marhabin da shirin gudanar da sabbin zabubbuka a zaman matakin da ya dace.

XS
SM
MD
LG