Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Zabi Hamid Karzai A Matsayin Shugaban Kasar Afghanistan - 2002-06-14


Babbar majalisar shawarwari ta Loya Jirga ta kasar Afghanistan, ta zabi shugaban gwamnatin rikon kwarya, Hamid Karzai, a matsayin sabon shugaban kasar.

Wannan kuri'a da aka yi jiya alhamis a birnin Kabul, ta zo a daidai lokacin da majalisar ke ci gaba da kokarin dinke barakar da aka samu a sanadin yaki, da gabar kabilanci da kuma talauci na tsawon shekaru ashirin.

Mr. Karzai zai shugabanci gwamnatin rikon kwarya wadda zata jagoranci kasar Afghanistan na watanni 18, watau shekara daya da rabi, dake tafe.

Mr. Karzai ya lashe kuri'u dubu daya da dari biyu da casa'in da biyar, daga cikin kuri'u dubu daya da dari biyar da aka kada.

Ba tare da jinkiri ba, Amurka ta taya sabon shugaban na Afghanistan murna.

A yanzu, majalisar ta Loya Jirga, zata maida hankalinta ga zaben wakilan majalisar zartaswa, da irin gwamnatin rikon kwaryar da za a kafa.

XS
SM
MD
LG