Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Shugaba Bush Ya Yaba Da Karshen Yarjejeniyar Haramta Kera Makaman Harbo Makamai Masu Linzami - 2002-06-14


Shugaba Bush yayi marhabin da ganin karshen yarjejeniyar haramta kera makaman harbo makamai masu linzami ta shekarar 1972, yana mai yin alkawarin kerawa da girka makaman da zasu kare Amurka daga harin makamai masu linzami ba tare da jinkiri ba.

A cikin wata sanarwa, Mr. Bush ya ce a yanzu Amurka zata iya fuskantar barazanar 'yan ta'adda da kasashe masu neman ganin bayanta.

Yarjejeniyar ta ABM ta 1972, ta haramta kerawa ko girka makaman da zasu iya kare kasa daga makamai masu linzami. A cikin wata Disambar bara, shugaba Bush ya bada sanarwar wata 6 da ake bukata ta janyewa daga cikin yarjejeniyar, yana mai bayyana ta a zaman ta zamanin zaman gabar akida.

Jami'an kasar Rasha sun bayyana takaicin ganin rushewar wannan yarjejeniya, yayin da suka yi alkawarin hada kai da Amurka a fannin tsaron kai daga makamai masu linzami.

XS
SM
MD
LG