Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Bush Ya Umurci Hukumar Leken Asirin Amurka Da Ta Hambarar Da Saddam Hussein Daga Kan Mulki - 2002-06-17


'Yan majalisar dokokin Amurka, sun ce suna goyon bayan wasu shirye-shirye masu yawa da sarkakiya, wadanda gwamnatin Amurka take yi na tsige shugaban Iraqi, Saddam Husseini, daga kan mulki.

A wasu hirarrakin da aka yi da su jiya a gidajen telebijan na nan Amurka, 'yan majalisa daga jam'iyyar "Republican" da takwarorinsu na jam'iyyar "Democrat" sun halalta tsare-tsaren da aka yi, ta hanyar bada misali da zargin da ake yi wa gwamnatin Iraqi a birnin Bagadaza, na kokarin mallakar makaman kare-dangi.

Jaridar Washington Post, bugun jiya lahadi, ta bada rahoton cewa shugaba Bush ya bada umurnin cewa, a ci gaba da sa himma, a wani makircin da ake yi a asirce, wanda ya hada da hukumar leken asirin Amurka ta C-I-A, domin a tunbuke shugaban na Iraqi daga kan mulki.

Wannan labari da aka buga a shafin farko na jaridar ya ce, tun a farkon wannan shekarar ce, Mr Bush ya sanya hannu akan wata takardar umurni ta shugaban kasa wadda ta bukaci da a karfafa goyon bayan da ake baiwa kungiyoyin adawa na Iraqi, sannan kuma a fadada dabarun tara bayanan leken asiri gameda sojojin kasar, da sauran hukumomin tsaronta.

XS
SM
MD
LG