Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Bafalasdine Ya Kashe 'Yan Kama-Wuri-Zauna Su Biyar A Yammacin Kogin Jordan - 2002-06-21


Wani Bafalasdine dan bindiga ya saci jiki ya shiga cikin wata unguwar kama-wuri-zauna ta Yahudawa a Yammacin kogin Jordan, inda ya harbe mutane biyar har lahira, cikinsu har da wata mata da 'ya'yanta uku.

Mutane takwas sun ji rauni a wannan harin da aka kai cikin unguwar share-ka-zauna ta Itamar dake bangaren arewacin Yammacin kogin Jordan.

Rundunar sojan Isra'ila ta ce har ila yau dan bindigar ya kashe wani mai gadi, kafin 'yan sandar bakin iyaka na Isra'ila su bindige, su kashe shi.

Kungiyar kwatar 'yancin Falasdinu ta "PFLP" ta dauki alhakin kai wannan harin.

falasdinawa shaidu sun ce tankokin yakin Isra'ila da sojojinsu sun nausa cikin birnin nablus kafin ketowar alfijir, a wani mataki na maida martanin wannan harin.

Harin da aka kai cikin unguwar yahudawan, ya zo a bayan da Isra'ila ta fara kiran sojojinta na wucin gadi da su shiga cikin damara, bayan da ta umurci sojojinta da su koma su mamaye wasu garuruwa biyar a yankin Yammacin kogin Jordan. Wannan umurni ya biyo bayan hare-haren bam biyu na kunar-bakin-wake da Falasdinawa suka kai suka kashe 'yan Isra'ila 26 a Qudus.

Tun fari a jiya alhamis, shugaban Falasdinawa, Yasser Arafat, ya roki kungiyoyin Falasdinawa da su kawo karshen dukkan hare-hare a kan fararen hula 'yan Isra'ila. Ya ce babu abinda hare-haren ke haddasawa im ban da bai wa Isra'ila dalili na neman mamaye yankunan Falasdinawa.

XS
SM
MD
LG