Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Shugabannin Afirka Zasu Gana A Ethiopia Kan Rikicin Madagascar - 2002-06-21


Shugabannin Afirka zasu gudanar da wani taron koli yau Jumma'a a kasar Ethiopia, a wani yunkurin kawo karshen rikicin siyasar da aka shafe watanni shida ana yi a tsibirin Madagascar.

Ana sa ran cewa shugaba Levy Mwanawasa na Zambiya da shugaba Abdoulaye Wade na Senegal, sune zasu shugabanci wannan taro da Kungiyar Hada Kan Kasashen Afirka ta shirya.

Ba a tabbatar da ko shugaban Madagascar na yanzu, Marc Ravalomanana, da kuma tsohon shugaban kasar, Didier Ratsiraka, zasu halarci wannan taron ba.

Wannan rikicin siyasa da ya samo asali daga gardamar sakamakon zaben shugaban kasa da aka yi a watan Disamba, ya hana kai mai zuwa manyan biranen kasar, ya kuma dakatar da jigilar kayayyakin abinci a fadin kasar.

XS
SM
MD
LG