Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Bush Yana Son A Gaggauta Amincewa Da Yarjejeniyar Nukiliya - 2002-06-21


Shugaba Bush ya nemi majalisar dattijai da ta gaggauta amincewa da yarjejeniyar rage makaman nukiliyar da ya cimma da kasar Rasha a watan da ya shige.

A jiya shugaban na Amurka ya gabatar da daftarin wannan yarjejeniya ga majalisar domin neman amincewarta, yana mai fadin cewa zxata gabatar da wani sabon zamani na hada kai da tsohuwar abokiyar gabar Amurka, tare da kara tabbatar da tsaron duniya.

A ranar 24 ga watan mayu shugaba Bush da takwaransa na Rasha, Vladimir Putin, suka rattaba hannu kan yarjejeniyar a birnin Moscow.

Yarjejeniyar ta bukaci kasashen biyu da su rage kashi biyu cikin uku na makaman nukiliyar da suka mallaka, su komo zuwa kundoji dubu daya da dari bakwai, zuwa dubu biyu da dari biyu wadanda kowaccensu zata iya girkawa.

XS
SM
MD
LG